Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- kasar Iran ya nakalto kwamitin kimiyya da fasaha ta kungiyar ‘Stat Nano’ ta gudanar da bincike a tsakanin kasashe 25 a duniya dangane da ci gaba a samar da ilmi da kayaki a bangaren fasahar nano, inda ta gano cewa cibiyar bincike na fasahar nano ta kamfanin man fetur na kasar Iran ce a gaban a duniya da kasha 41.94%.
Labarin ya kara da cewa biye da ita sai kasar kamfanin ‘oil Corporation na kasar India da kasha 13% sai kuma na uku kamfanin SK na kasar Korea ta Kudu tare da kasha 11%.
Daga karshe kungiyar ‘Stat Nano’ ta kammala da cewa binciken nasu ya hada da wasu manya-manyan kamfanoni a kasashen Turai da Amurka daga cikin kasashe 25 da ta zaba.
342/